IQNA

23:49 - March 02, 2020
Lambar Labari: 3484578
Tehran (IQNA) Sabuwar dambawar siyasa ta kabilanci da nuna bambanci da wariya ga musulmi a kasar India.

Siyasar kasar India a matsayin daya daga cikin kasashe masu mulkin dimukradiyya da suke da yawa jama’a a duniya na babban tasiri a siyasar duniya baki daya, a irin wanann lokacin ne kasar ta samar da dokar wariya ga wani bangare na mabiya addini a kasar da ke da al’ummomi da kabilu 72 a cikinta.

Kundin tsarin mulki

Bisa gat sari na kasar Indi, wanda kuma shi ne a mafi yawan kasashen dniya, kundin tsarin mulki kasa yana a matsayin abin dogaro ga kowane dan kasa, wajen kare hakkokinsa a matsayinsa na dan kasa, a kan haka ne ma tutar kasa da taken kasa suke a matsayin abin da kundin tsarin mulki ya tababtar da su domin hada kan ‘yan kasa.

Bambancin Ra’ayi Da Mahanga

Wasu daga cikin yankunan kasar India musamman yankunan arewa maso gabashin kasar wadanda akasarinsu musulmi ne, da dama daga cikinsu suna da sabani da mahangar gwamnatin kasar ta yanzu kan yadda take yin ta’ammuli da sha’anin musulmi.

Danne Hakkokin Marassa Rinjaye

Kasantuwar msuulmi marassa rinjaye a kasar India, baya nufin cewa kuma su tsiraru ne, domin kuwa adadin musulmin kasar ya tasamma kusan kashi ashirin cikin dari na mutanen kasar, wanda kuma akwai wasu addinan da ba su wuce kashi biyu cikin dari ba, amma du da haka ana la’akari da musulmi a matsayin su ne ‘yan tsiraru marassa gata a kasar.

Yunkurin Haiifar Da Yaki Kan Musulmi

Sakamakon matakin da gwamnatin kasar India ta dauka na kirkiro sabuwar dokar nuna wariya ga musulmi, da kuma yadda musulmin kasar suka nuna rashin gamsuwarsu da hakan, wannan yasa mabiya addinin Hindu masu tsatsauran ra’ayi suka dauki doka a hannunsu, wajen yin kisan gilla a kan msuulmi, tare da lalata dukiyoyi da kadarorin musulmi, ba tare da gwamnatin kasar ta nuna wata damuwa ko daukar matakin kare rayukan musulmin ba, inda aka kashe mutane 39 a rikicin makon nan.

Sabuwar Dokar Zama Dan Kasa Babban Kalu Bale Ga Dimukradiyar India

Sabuwar Dokar Zama Dan Kasa Babban Kalu Bale Ga Dimukradiyar India

Sabuwar Dokar Zama Dan Kasa Babban Kalu Bale Ga Dimukradiyar India

3882645

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: India ، musulmi ، muslunci ، wariya ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: