IQNA

Nasihohin Jagora Dangane Matakan Kare Kansu Daga Kamuwa Da Cutar Da Ke Yaduwa

23:43 - March 03, 2020
Lambar Labari: 3484580
Tehran – (IQNA) jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya gabatar da wasu nasihohi ga al’ummar kasar kan wajabcin daukar matakan ad suka dace domin su kare kansu daga kamuwa da cutar corona.

Shafin jagora ya ayar da rahoton cewa, Jagoran juyin juya halin musulunci Ayatullahi Sayyeed Ali Khamenei ya bukaci dukkan mutanen Iran su yi aiki da umurnin jami’an kiwon lafiya na kasar don hana kamuwa da kuma yaduwar cutar Corona wacce ake fama da ita a mafi yawan lardunan kasar.

Kamfanin dillancin labaran Mehr ya nakalto jagoran yana fadar haka a safiyar yau Talata, bayan ya shuka itatuwa biyu a ranar shuka itatuwa ta kasa a gidansa.

Har ila yau jagoran ya yaba da yadda jami’an kiwon lafiya da kuma wadanda suke taimaka masu don ganin bayan wannan cutar.

Ya kuma bukaci dukkan ma’aikatu da hukumomi wadanda suka hada da sojojin kasar da kuma wadanda suke karkashin ofishinsa da su bada dukkan taimakon da ma’aikatar lafiya zata bukata a wajensu don ganin bayan wannan annobar.

Haka nan kuma ya bukaci duk wadanda suke iya bada wani taimako don yaki da wannan annobar su yi hakan.

Ban haka ya ce yin addu’a da kuma rokon Allah ya kawo karshen wannan annobar yana da matukar muhimmanci.

Jagoran ya bayyana kokarin da jami’an kiwon lafiya suka yi a wannan bangaren a matsayin jihadi kan tafarkin Allah ya kuma roki Allah ya gafartawa wadanda suka rasa rayukansu sanadiyyar cutar, ya kuma bawa wadanda suka kamu da ita lafiya, a ko ina suke a duniya baki daya.

3882908

 

captcha