IQNA

Kadan Daga Cikin Tarihin Imam Ali (AS)

19:36 - March 07, 2020
4
Lambar Labari: 3484595
Tehran (IQNA) wani bangare daga cikin rayuwar Imam Ali (AS) daga lokacin kuruciyarsa, da kuma tarbiyar da ya samu a wannan lokaci a hannun manzon Allah (SAW).

Bayan da Imam Ali (a.s.) ya cika shekara shida da haihuwa, kulawarsa ta koma ga hannun Manzon Allah (s.a.w.a.) ta gaba daya, ma'ana ya koma gidan Ma'aikin Allah (s.a.w.a) da zama ya bar ainihin gidan iyayensa.

Akwai maganganu daban-daban kan yadda wannan lamari ya faru.

Wasu suna cewa shi Ma'aikin Allah (s.a.w.a) da kansa ne ya bukaci Abu Talib da ya ba shi Aliyu (a.s.) don ya saukaka masa rayuwa, kamar yadda Abu Rafi ya ruwaito cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya tafi wajen Abu Talib yace masa: Ya Baffana, ni ina son ka bani wani daga cikin 'ya'yanka don ya taimaka min cikin al'amarina, sannan kuma ni ma in yaye maka wahalar da kake fuskanta. Sai Abu Talib yace masa: Dauki duk wanda ka ke so. Don haka sai ya dauki Aliyu.

Wasu kuma cewa suka yi mahaifiyarsa Fatima bint Asad (r.a) ce da kanta ta bai wa Manzon Allah (s.a.w.a.) Imam Ali (a.s.), hakan kuwa don ta cika alkawarin da ta yi ne na ba shi duk wani abin da ta haifa lokacin tana da ciki.

Koda yake abin da yafi shuhura dangane da wannan lamari shi ne cewa, a wannan shekarar mutane Makka sun fuskanci tsananin masifar fari, al'amarin da ya sanya su cikin wahala da kuma damuwa. To wannan lamari kuwa ya sanya Abu Talib (r.a) cikin wahala ta gaske kasantuwan shi mutum ne mai yawan iyali kuma ga shi ba shi da wani abin hannu.

 

To don yaye masa wannan wahala, sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya tafi wajen baffansa Abbas (wasu kuma ma suka ce har da Sayyidina Hamza, yace masa: "Ya Baffana, ka san cewa Abu Talib mutum ne mai yawan iyali kuma ga wahalar da yake ciki saboda abin da ya sami mutane, don haka zo mu je gurinsa kowannenmu ya dauki guda daga cikin 'ya'yayensa don mu saukake masa wannan wahala". Nan take kuwa ya yarda da wannan shawara ta Annabi (s.a.w.a.), don haka sai suka tafi wajen Abu Talib don shaida masa wannan kuduri nasu.

 

Shi kuwa sai yace musu, idan dai har za su bar masa Akil (daya daga cikin 'ya'yayen nasa), to su dauki duk wanda suke so. Wasu kuma suka ce cewa yayi, idan har za su bar masa Akil da Talib, to su dauki duk wanda suke so.

 

Don haka sai Annabi (s.a.w.a.) ya dauki Imam Ali (a.s.) shi kuma Abbas ya dauki Ja'afar. Su kuma wanda suka ce har da Sayyidina Hamza (r.a) a ciki, cewa suka yi Hamza shi ne ya dauki Ja'afar, shi kuma Abbas ya dauki Talib kana shi kuma Annabi (s.a.w.a.) ya dauki Imam Ali (a.s.).

To koma dai menene, kulawan Imam Ali (a.s.) dai ta koma hannun Annabi (s.a.w.a.), inda yaci gaba da kulawa da shi da shayar da shi daga tafkin annabci.

Kulawa irin ta gidan annabci yana mai shayar da shi da hikima, ilimi, kyawawan dabi'u, karimci da jarunta, duk dai irin ta annabci. A saboda haka ne ma ya kere kowa a duk fadin duniya a dukkan bangarori na rayuwa da kuma daukaka.

Don kuwa shi ya kasance tare da Manzon Allah (s.a.w.a.) tun farkon rayuwarsa har zuwa karshenta, bai taba rabuwa da shi ba.

A duk tsawon wannan lokaci na rayuwarsa, Annabi (s.a.w.a.) ya kaddamar da dukkan abin da zai iya wajen baiwa Imam Ali (a.s.) tarbiyya wacce babu wani mahaluki da ya taba samun irinta, ta yadda yayi fintinkau wa dukkan sauran halittu na duniya.

Ya samu irin wannan kyakkyawar tarbiyya ta yadda har ya zamanto babu wani wanda zai gudanar da aikin da Manzon Allah (s.a.w.a.) zai yi in ba shi ba (kamar yadda zamu gani nan gaba). Sannan kuma ya zamanto ya sami tarbiyya irinta Ubangiji ta yadda babu wani da ya cancanci ya zamanto wasiyi kana kuma halifan Annabi (s.a.w.a.) a bayansa in ba shi ba.

Sannan shi kuma Annabin (s.a.w.a.) a nasa bangaren ba shi da wani wanda ya cancanci ya ba shi wannan sirri na Ubangiji in ba shi ba.

Hakika wannan dan karamin littafi, ko kuma shi kansa mai rubuta shi, ya gaza ya bayyana irin wannan tarbiyya da kuma matsayin da Imam Ali (a.s.) yake da shi a wajen Annabi (s.a.w.a.) da kuma irin tarbiyyar da ya samu a wajensa, don kuwa babu shakka wannan wani al'amari ne na Ubangiji.

Wanda Aka Watsa: 4
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
NAJIB Amiru
3
10
Muna God I ya Allah ya saka
Amsoshi
Ba A San Shi Ba
Mam bash bamalli. Allah yasaka da alkairi
Ba A San Shi Ba
Allah yaka.ra ƴada agare ameen
inusa saidu
0
0
in son shiga shi a
captcha