IQNA

23:58 - March 08, 2020
Lambar Labari: 3484601
Tehran (IQNA) Jaridar Middleast ta bayar da bayanin cewa ya zuwa yanzu ‘ya’yan gidan sarauta 20 ne Muhammad Bin Salman ya bayar da umarnin kame su.

Jaridar ta bayyana cewa, Muhammad Bin Salman yarima mai jiran gadon masarautar kasar ta Saudiyya, ya bayar da umarnin kame ‘ya’yan gidan sarautar ne bisa zarginsu da yake yi da yunkrin juyin mulki.

Bisa ga wannan rahoto, daga cikin wadanda aka kame akwai Ahmad bin Abdulaziz dan uwa shakiki ga sarkin kasar Salman Bin Abdulaziz, kamar yadda kuma aka kame dansa Naif bin Ahmad bin Abdulaziz, sai kuma Muhammad Bin Naif tsohon yarima mai jiran gado, da kuma dan uwansa Nawaf bin Naif.

Kafin wannan lokacin dai a ranar Asabar da ta gabata, jaridar ta wall Street Journal ta bayar da rahoton kame yarima Ahmad Bin Abdulaziz dan uwa shakiki ga sarki Salman, da kuma Muhammad bin naif, tsohon yarima mai jiran gado, da kuma dan uwansa Nawaf bin Naif, amma cikin kasa da kawana guda, Muhammad Bin Salman ya bayar da umarnin kame karin wasu daga cikin 'ya'yan gidan sarautar kasar.

 

3883898

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Saudiyya ، ، ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: