IQNA

22:32 - March 11, 2020
Lambar Labari: 3484610
Tehran (IQNA) yau falastinawa da dama ne suka fita cikin hayyacinsu, biyo bayan antaya musu hayaki mai sanya hawaye da ‘yan sanda yahudawa suka yia  yankin Nablus.

Kamfanin dullancin labaran Anadolu ya bayar da rahoton cewa, a yau jami’an ‘yan sandan yahudawan Isra’ila sun yi amfani da karfi wajen tarwatsa gungun Falastinawa da suka taru a  gefen matsugunnin yahudawa ‘yan share wuri zauna na Jabal Al’ma’arrah.

Rahotanni sun ce ‘yan sandan yahudawan sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye fiye da kima a kan fararen hula falastinawa da suka taru a wurin, inda wasu daga cikinsu suka suma, wasu kuma suka samu raunuka, kamar yadda kuma aka kwashi wasu zuwa asibitocin da ke kusa da yankin domin ceto rayuwarsu.

Matsugunnin Jabal Al’ma’arrah dai yana daga cikin yankunan falastinawa da Isra’ila ta kwace da karfin bindiga tare da rushe dukkanin gidajen falastinawa da wurin, domin gina matsugunnin yahudawa ‘yan share wuri zauna da suke yin hijira zuwa Isra’ila daga kasashen duniya.

3884646

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: