IQNA

23:54 - March 15, 2020
Lambar Labari: 3484626
Tehran (IQNA) sakamakon fashewar wasu abubuwa a cikin jihar Lagos da ke Najeriya akalla mutane 15 sun rasa rayukansu wasu kuma sun jikkata.

Hukumar da take kula da ayyukan agajin gaggawa ta Najeriya ce ta sanar da afkwuar hastari a yankin Abule Ado, a kusa da kasuwar baje koli akan babbar hanyar da ta hada Lagos zuwa Badagry

Jami’i mai kula da ayyukan hukumar agajin gaggawar a Lagos, Mr.Ibrahim Farinloye ya ce a halin yanzu ba a kai ga tantance musabbabin hatsarin ba, ko kuma adadin asarar rayukan da aka samu, domin ana ci gaba da aiki ceto da kuma bincike a yankin da lamarin ya faru.

Mr.Ibrahim ya kara da cewa an sami tashin gobara saboda fashewar abubuwan wanda kuma ya shafi bututun man fetur, sai dai tuni kamfanin man fetur na kasar ya rufe kwararar mai a cikin bututun a matsayin rigakafi.

 

 

3885655

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Lagos ، abu ، lamarin ، fashewar ، fetur ، hukumar agaji ، Najeriya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: