IQNA

23:58 - March 18, 2020
Lambar Labari: 3484633
Tehran (IQNA) dakarun kasar Yemen sun samu nasarar kammala kwace iko da lardin Jauf daga hannun sojojin hayar Saudiyya.

Mai Magana da yawun sojojin kasar ta Yemen, Yahya Sari’i ne ya bayyana haka a yau Talata yana mai kara da cewa; Yankuna kadan ne su ka rage a dukkanin gundumar ta Jauf, wadanda ba a kai ga ‘yanto su ba.

Yahya Sa’ri’i, ya ci gaba da cewa; yankuna da ba a ‘yanto da su ba su ne; Khab, Saharar Hazm,da yankin Sha’af.

Sojojin na Yamen tare da dakarun sa-kai na”Ansarullah” ne dai su ka kai gagarumin farmaki a yankin wanda ya kai ga ‘yanto shi daga ‘yan koren Saudiyya.

Yahya Sari’i ya kara da cewa; Kwanaki biyar aka dauka an kwami a tsakanin sojoji da dakarun sa-kai a gefe daya da kuma ‘yan koren Saudiyya a daya gefen.

Tun a 2015 ne dai kasar Saudiyya ta kafa kawancen da ya shelanta yaki akan kasar Yemen da al’ummarta wanda ya zuwa yanzu ya ci dubban rayuka da kuma jikkata wasu dubun dubata.

Har ila yau, hare-haren na Saudiyya sun yi sanadin rushewar cibioyoyin kiwon lafiya a fadin kasar ta Yemen.

 

3886166

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: yemen ، hari ، lardin Jauf ، dakarun sa kai ، na kasar
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: