IQNA

Takunkumin Amurka Kan Iran Babban Zalunci Ne

23:59 - March 21, 2020
Lambar Labari: 3484644
Takunkumin Amurka Kan Iran Babban Zalunci Ne
Tehran (IQNA) ‘Yar majalisar dokokin Amurka musulma Ilhan Omar ta bayyana takunkumin da gwamnatin Amurka take ci gaba da kakaba wa Iran da cewa zalunci ne.

A cikin wani bayani da ta rubuta a shafinta na twitter, Ilhan Omar ta bayyana cewa; takunkumin Amurka yana da babban tasiri wajen cikas ga yunurin Iran an murkushe cutar Corona a kasar, a daidai irin wannan lokacin ne kuma gwamnatin Amurka take kara tsananta takunkumin, ta ce wannan shi ne zalunci mafi girma.

Ta ci gaba da cewa, baya ga takunkumi a bangaren kayayyain kiwon lafiya, shi ma takunkumin tattalin arzikin Amurka a kan kasar wani nau’i ne na zalunci.

A ranar Alhamis da ta gabata ce Amurka ta sanar da kara tsananta takunkuminta akan Iran, biyo bayan kiraye-kirayen da bangarori na duniya suka yi wa Amurka, na janye takunkumanta akan kasar ta Iran, domin samun sauki yaki da cutar corona.

3886742

 

captcha