IQNA

23:18 - March 22, 2020
Lambar Labari: 3484647
Tehran (IQNA) mabiya addinin musulunci a birnin Birmingham na kasar Burtaniya suna kokarin sulhunta tsakanin jama’a masu sabani a birnin.

Jaridar Independet ta kasar Burtaniya ta bayar da rahoton cewa, babban masallacin juma’a na brnin Birmingham na Sultan Bahu ya bullo da sabbin shirye-shiye na kyautata zamantakewa tsakanin jama’a, inda aka kafa kwamiti na mutane 150 domin gudanar da shirin.

A cikin watanni hudu da suka gabata an samu matsaloli 269 da suka shafi sare-sae da wukake, wannan ne yasa musulmi suka dauki wannan mataki sakamakon yadda ake samun matsaloli a tsakanin jama’a musamman ma matasa a birnin, inda har wasu kan yi amfani da wukake wajen yankar abokan hamayyarsu.

Daga shekara ta 2014 ya zuwa yanzu ayyukan laifuka sun karua  yankin West Midlands, inda akasari kuma laifuka ne mana da suke da alaka da amfani da wukake, wanda kuma shirin da musulmin suke da shi zai taimaka wajen sasanta masu husuma.

3886873

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: watanni ، zaantakewa ، amfani ، abokan hamayya ، matsaloli ، matasa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: