IQNA

23:58 - March 24, 2020
Lambar Labari: 3484653
Tehran (IQNA) an kafa dokar hana kai komo a dukkanin biranan kasar Masar na wasu lokuta, domin kace wa yaduwar cutar corona a cikin kasar.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, firayi ministan kasar Masar Mustafa Madbuli ya bayyana cewa, daga ranar Laraba dokar hana fita daga gidaje da aka kafa za ta fara aiki.

Ya ce wannan doka za ta kasance ne daga kimanin karfe 7 na dare zuwa karfe 6 na safe dole mutane su zauna cikin gidajensu.

Haka nan kuma ya jaddada cewa, duk wani aiki na saba wannan doka zai fuskanci martani daga jami’an tsaro.

Madbuli ya ce tun kimanin makonni biyu da suka gabata ne dai aka dakatar da karatu a dukkanin makarantu da jami'oin kasar, kuma an kara kuma za su gaba da kasancewa a rufe ha zuwa wasu makonni biyu a nan gaba.

Ya zuwa yanzu dai Masar ta bayar da kudi da suka kai kimanin dala miliyan 63 ga ma'aikatar kiwon lafiya domin ayyukan yaki da corona.

Mutane 366 ne suka kamu da cutar a fadin kasar Masar, yayin da 19 daga cikinsu suka rasa rayukansu.

 

3887240

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Masar ، karfe ، fuskanci ، ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: