Jaridar Al’ahad ta bayar da rahoton cewa, Hussain namir jami’in Hizbullah a yankin Biga a kudancin Lebanon ya bayyana cewa, mambobin Hibullah 3,530 ne suke gudanar da ayyukan taimakon jama’a na yaki da corona a yankin.
Ya ce 266 jami’an kiwon lafiya ne, da suka hada da likitoci da ma’aikatan jinya da sauransu.
Haka nan kuma akwai motocin daukar marassa lafiya 20 da kungiyar ta tanada domin daukar marassa lafiya domin kai su asibiti.
Baya ga haka kuma kungiyar Hizbullah ta kafa wasu asibitoci an tafi da gidanka guda 13 domin kula da lafiyar mutane kyauta, haka nan kuma a bayanin ya ce kungiyar ta bayar da abinci ga iyalai dubu 22 a yankin, kuma shirin zai ci gaba.