IQNA

Isra'ila Na Tsoron Kada Ta Kasa Cika Shekaru 80 / Bayyanar Imam Mahdi Alkawali Ne

23:53 - April 08, 2020
Lambar Labari: 3484691
Tehran (IQNA) Babban Magatakardar Kungiyar Hizbullah Ta Lebanon Ya Jinjina wa Likitocin Kasar Saboda Yadda Su Ke Fada Da Cutar Corona.

Sayyid Nasrallah wanda ya gabatar da jawabi a jiya Talata dangane da zagayowar ranar 15 ga watan Sha’aban,ya yi godiya ga dukkanin bangarorin gwamnatin kasar musamman likitoci saboda rawar da su ke takawa wajen fada da cutar;”Corona”

A cikin jawabin nashi, Sayyid Nasrallah ya kara da cewa; Na sami sakwanni daga kungiyoyin likitoci musulmi da masu ayyukan jiyya a cikin asibitocin Lebanon da kuma dalibai masu karatun ayyukan likitanci daga kasashen waje, suna yin magana da harshe irin na mayaka da suke filin daga na sadaukar da kai da zama cikin shiri domin fuskantar kalubale.

Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah, Sayyid Nasrallah ya kuma kara da cewa; A halin da ake ciki a yanzu,likitoci da masu ayyukan jiyya su ne a sahun gaba na filin dagar fada da corona, suna kuma sadaukar da kawukansu da fuskantar hatsaruka wajen yin hakan.

Wani sashe na jawabin Sayydi Nasrallah, ya tabo zagayowar ranar shahadar Sayyid Muhammad Bakir Sadar na Iraqi wacce ita ce ranar 9 ga watan Aprilu tare da ‘yar’uwarsa Sayyidha Aminatu Sadr.

Sayyid Nasrallah ya kara da cewa; Sayyid Bakir ya kaddamar da hidima mai yawa wajen kare addinin musulunci, kuma ayyukan da ya yi tun wancan lokacin suna ci gaba a duniyar musulunci.

 

3890010

 

captcha