IQNA

Wani Likita Musulmi Ya Rasu A Kasar Burtaniya Bayan Kamuwa Da Corona

23:38 - April 10, 2020
Lambar Labari: 3484697
Tehran (IQNA) Abdulma’abud Shaudari daya ne daga cikin kwararrun likitoci a kasar Burtaniya ya rasu bayan kamuwa da cutar corona.

Jaridar Quds Alarabi ta bayar da rahoton cewa, Abdulma’abud ya rasu jiya a asibin queens da ke gabashin birnin Landan.

Rahoton ya ce kimanin makonni uku da suka gabata, ya bukaci firayi ministan kasar Burtaniya da hanzarta wajen ganin an samar da wadatattun kayan kayan aikin da likitoci masu kula da masu cutar corona suke bukata, musamman takunkuman rufe fuska da safar hannu masu dauke da sanadarai na magani.

Ya ce babbar matsalar da suke fuskanta wajen kula da masu dauke da cutar corona ita ce, ba su da wadatattun kayayyakin da suke bukata domin kare kansu a lokacin kula da marassa lafiya, wanda hakan a cewar Abdulma’abud zai iya jefa rayuwar likitoci da ma’aikatan kiwon lafiya cikin hatsari, wanda kuma bayan ako guda da wannan furuci ne cutar corona ta kamashi, bayan makonni biyu kuma ya rasu.

3890523

 

 

 

captcha