A cikin wani rahoto da shafin arabi 21 ya buga, ya bayyana cewan Mu’utaz Qutub ya sanar a shafinsa na twitter cewa, mahaifinsa Sheikh Jamal Qutub ya rasu, kuma an gudanar da janazarsa ba tare da tara mutane ba, saboda matsalolin da ake ciki, inda iyalansa da danginsa ne kawai suka halrci wurin.
Ya kirayi sauran al’ummar musulmi da su sanya mahaifinsa a cikin addu’a, kan Allah madaukakin sarki ya gafarta masa.
A cikin makonnin da suka gabata dai an ga Sheikh Jamal Qutub a cikin wani hoton bidiyo da ake yadawa, inda yake rokon Allah daya kawo wa al’ummar musulmi da ma sauran al’ummomin duniya baki daya karshen annobar corona.