IQNA

Kashi 40% Na Yhaudawa Da Suka Kamu Da Corona A Isra’ila Sun Zo Daga Amurka Ne

23:54 - April 15, 2020
Lambar Labari: 3484714
Tehran (IQNA) ma’aikatar kiwon lafiya ta Isra’ila ta sanar da cewa fiye da yahudawa dubu 12 ne suka kamu da cutar corona a halin yanzu.

Shafin yada labarai na alwaqt ya bayar da rahoton cewa, ma’aikatar kiwon lafiya ta Isra’ila ta sanar da cewa fiye da yahudawa dubu 12 ne suka kamu da cutar corona kuma kashi 40% daga cikinsu sun zo ne daga Amurka.

Bayanin ya kara da cewa, daga cikin yahudawan da suka kamu da cutar kashi 15% sun kamu da ita ne a wurare na hada-hadar jama’a.

Ma’aiklatar kiwon lafiyan Isra’ila ta bayyana cewa, babban dalilin da ya jawo kamuwar mutane da yawa ita ce tun a farkon watan Maris ba a saka Amurka a cikin kasashen da aka hana zuwa ba domin kaucewa kamuwa da cutar.

Yanzu haka wasu daruruwan yahudawan ad suka kamu da corona, suna yin lumfashi ne kai tsaye ta hanyar na’urori.

3891912

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: yahudawa ، kamu da ، cutar corona ، sun zo ، Amurka ، kaucewa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha