Kamfanin dillancin labaran kasar Lebanon ya bayar da rahoton cewa, a jiya wasu jiragen Isra’ila marassa matuki sun keta hurumin sararin samaniyar birnin Beirut na kasar.
Gwamnatin kasar Lebanon ta fitar da bayani a yau inda ta yi Allawadai da kakkausar murya akan wannan shisshigi na gwamnatin yahudawa akan kasarta.
Haka nan kuma gwamnatin ta Lebanon ta shirya wata wasika ga babban sakataren majalisar dinkin duniya, inda ta yi karar gwamnatin yahudawan, tare da yin kira da a dauki mataki kan hakan.