IQNA

‘Yan Sanda Afirka Ta kudu Sun Baiwa Musulmi Hakuri Kan Cin Zarafin Da wani Dan Sanda Ya yi

23:48 - April 27, 2020
Lambar Labari: 3484750
Tehran (IQNA) ‘yan sandan kasar Afirka ta kudu sun baiwa musulmi hakuri lan cin zarafin da wani dan sanda ya yi a kan addinin musulunci.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa,a  cikin wani bayani da ya fitar babban sufeton ‘yan sanada  akasar Afirka ta kudu ya nuna damuwa kan kalaman dawani dan sanda ya yi a kan manzon Allaha  kasar.

Bayanin ya ce a madadin rundunar ‘yan sanda ta kasar Afirka ta kudu, babban sufeton ‘yan sanda na kasar yana baiwa dukkanin musulmin kasar hakuri.

A ranar Asabar da ta gabata ce wasu ‘yan sanda suka kama wasu musulmi sakamakon saba dokar hana zirga-zirga, inda suka fito suna yin salla a masallaci, a daidai lokacin da aka hana yin hakan ga dukkanin mabiya addinai na kirista komusulmi ko wasu addinai na daban.

A cikin wani bidiyo da ak adauka  a lokacin kama musulmin, wani dan sanda ya rika fadin cewa shin kun fi shugaban kasa ne? ko kuwa manzon naku ya fi shugaban kasar nan ne, da har zai kafa doka ku karya?

Kasar Afirka ta kudu dai ita ce ta daya wajen yawan wadanda suka kamu da corona inda yawan kamuwar ya kai dubu 4 da 546, sai kuma mutane 78 da suka mutu sakamakon hakan.

Musulmin Afirka ta kudu su ne kashi 3.5 na dukkanin mutanen kasar wada yawansu ya kai miliyan 57.

3894544

 

captcha