IQNA

Rouhani: Dole A Dauki Matakai Na Kalubalantar Takunkuman Amurka

23:47 - April 28, 2020
Lambar Labari: 3484752
Tehran (IQNA) shugaba Rauhani na Iran ya jaddada wajabcin daukar matakan na bai daya tsakanin kasashe domin kalubalantar takunkuman Amurka da kuma kare al’ummar falastinawa.

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya bukaci hadin kai tsakanin kasashen Afirka ta kudu da kuma sauran kasashen duniya don kubutar da al’ummar Palasdinu daga zaluncin Amurka da kuma HKI.

Har’ila yau da kuma samar da hanyar warware rikicin kasar Siriya ta hanyar tattaunawa.

Shugaba Rouhani ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa a safiyar yau Talata ta wayar tarho.

Shugaban ya bukaci takwaransa na Afirka kan habaka dangantaka a harkokin kasuwanci da kuma na tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.

Har’ila yau Rouhani ya bukaci kasashen biyu su yi musayar bayanai kan dabarbarun yakar cutar Corona.

Daga karshe shugaban ya bukaci kasar Afirka ta Kadu a matsayin ta na mamba, na wucin gadi a kwamitin tsaro na Majalaisar Dinkin Duniya, ta yi kokarin kawo karshen son ran da Amurka take nuna wa a kwamitin tsaron. Musamman dorawa kasar Iran takunkuman tattalin arziki ba tare da amincewar sauran yan kwamitin ba.

 

3895019

 

 

 

 

 

 

captcha