IQNA

16:20 - May 08, 2020
Lambar Labari: 3484776
Tehran (IQNA) babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya yi tir da nuna kyama ga wasu mutane da sunan kyamar corona.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayaninsa da aka watsa  ayau Juma’a, babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya bayyana cewa, dole ne a kawo karshen wata fitina da take tasowa a duniya ta nuna kyama ga wasu mutane da sunan su baki ne, kuma ake danganta yaduwar cutar corona da su.

Ya ce sakamakon yaduwar Corona musulmi sun fuskanci matsala a wasu wurare, inda aka cutar da su da kuma gallaza musu saboda batun corona, amma ba tare da ya ambaci wata kasa takamaimai ba.

Guterres ya ce dole al’ummomin duniya su ajiye duk wani nau’i na kyama da nuna kiyayya ga ‘yan uwansu mutane, tare da nuna kauna da son juna da yada zaman lafiya, da gudanar da ayyukan jin kai da alhairi, ba tare da la’akari da kowane irin banbanci da ke tsakaninsu ba.

Kamar yadda ya nuna taaici kan yadda ake tsangwamar jami’an kiwon lafiya a wasu wurare, da kuma kungiyoyin kare hakkin bil adama gami da ‘yan jarida, ba domin komai ba, sai saboda suna gudanar da aikinsu, tare da sauke wajibin da ya rataya a kansu.

 

3897256

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: