Lokacin azumin watan Ramadan wata dama ce ga musulmin kasar Singapore ta yin ibada, da zama na karatun kur’ani da buda baki da salloli a masallatai. Amma a shekarar bana kamar sauran kasashen duniya, lokacin ya zo da annobar corona wadda ta kawo cikas ga lamurra da dama na rayuwar jama’a.