IQNA

22:58 - May 19, 2020
Lambar Labari: 3484814
Tehran (IQNA) Orhan Turgut wani mai daukar hoto ne dan kasar Turkiya wanda ya fayyace wurare 200 da aka ambata  a cikin kur’ani.

Shafin yada labarai na alrabi jaded ya bayar da rahoton cewa, wannan mai daukar hoto yana niyyar daukar hotunan wurare da aka mabata a cikin wadanda suke da samuwa.

Ya yi yawo a kasashen musulmi daban-daban domin duba wadannan wurare 200 da aka mabata a cikin kur’ani, ya kuma samu nasarar daukar hotunan wurare 40 daga cikinsu.

Bayan daukar hotunan yana aikin tsara su kafin fitar da su gaduniya domin sanin hikimar ubangiji madaukain sarki dangane da ambatar wadannan wurare.

Daga cikin kasashen da aka dauki hotunan wuraren da aka ambata a cikin kur’ani akwai Saudiyya, Jorda, Syria, masar da sauransu.

Bayan haka kuma ya dauki wasu hotuna a wasu wurare na muslucni da suke da tarihia  cikin wadannan kasashe, inda adadin hotuann da ya dauka  ayayin tafiyar tasa sun kai hotuna dubu 100 a jimlace.

3899956

 

Abubuwan Da Ya Shafa: ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: