IQNA

Kwamitin Makaranta Kur’ani A Masar Ya Dakatar Da Wani Jigo A Cikinsa

23:51 - May 27, 2020
Lambar Labari: 3484841
Tehran (IQNA) kwamitin makaranta kur’ani na kasar Masar ya dakatar da Salah Aljamal babban mamba a kwamitin saboda wani furuci da ake kallonsa a matayin cin zarafi ga manyan makaranta.

Jaridar yaum Sabi ta bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da kwamitin ya fitar ya bayyana cewa, Salah Aljamal ya bayyana kansa a matsayin mutum na farko a kasar Masar ta fuskar karatun kur’ani, tare da bayyana cewa kurakuransa daidai suke da na manya irin su Sheikh Khalil Husri da Sheikh Sadiq Minshawi da Abdulbasit da makamantansu.

Wannan furuci ya harzuka mtane da dama  a kasar ta Masar, inda suke ganin cewa bayyana knsa a matsayin na farko na nufin ya fifita kansa  a kan wadannan manyan makaranta na duniya baki daya, kuma hakan na a matsayin tozarta su ne.

Sheikh Muhammad Hashad shugaban kwamitin makaranta kur’ani na kasar Masar baki daya ya bukaci da a dakatar da Salah daga kwamitin, sannan a dauki matakai na bincike kan dalilan da suka sanya shi yin wannan furuci na ban mamaki.

Sai dai a nasa bangaren Salah ya bayyana cewa, baya da nufin wulakanta wani daga manyan makaranta na Masar domin dukkanins malamansa ne, kuma har yanz da su yake yin koyi, kuma albakacinsu yake ci, maganasa yana wasa ne domin a yi dariya kawai, amma matsayin manyan malaman kur’ani ya wuce tozarci.

 

3901486

 

captcha