IQNA

Kungiyoyi Da cibiyoyi 200 Na Duniya Sun Nuna Goyon Baya Ga Aqsa

23:53 - June 03, 2020
Lambar Labari: 3484858
Tehran (IQNA) kungiyoyi da cibiyoyi 200 daga kasashe 30 sun nuna goyon bayansu ga Aqsa.

Shafin yada labarai na arabi 21 ya bayar da rahoton cewa, kungiyoyin da kuma cibiyoyin za su fitar da bayani na hadin gwiwa karkashin wani kamfe na kare birnin Quds da masallacin aqsa.

A ranar 7 ga wannan wata na Yuni ne za a fitar da bayanin kungiyoyin da cioyoyin na hadin gwiwa daga kasashen duniya, wanda ranar ta yi da ranar da ake cika shekaru 53 da mamayar birnin Quds da kuma masallacin aqsa.

Za a fitar da bayanin ne a cikin harsuna 12 na duniya, da hakan ya hada da turancin Ingilishi da kuma Faransanci gami da larabci da kuma wasu harsunan.

Da da dama cikin wadannan kungiyoyin ba na musulmi ba ne, amma suna nuna goyon bayansu ga al'ummar Falastinu, da kuma yin tir da irin zaluncin da suke fuskanta a cikin kasarsu, kuma bayanain baki daya zai zo ne karkashin kamfe maitaken #WeStand۴AlQuds.

A ranar 7 ga watan Yuni za a gudanar da taruka a kasashen duniya daban-daban domin tunawa da ranar mamaye birnin quds.

 

 

 

 

3902837

 

captcha