IQNA

Falastinawa Na Goyon Bayan Masu Adawa Da Wariya

23:48 - June 11, 2020
Lambar Labari: 3484883
Tehran (IQNA) Al’ummar Falastinu sun bi sahun mutanen Amurka masu nuna adawa da siyasar nuna wariya a tsakanin ‘yan adam.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, wasu falastinawa masu fasahar zane sun yi zane-zane a kan katangar wariya da Isra’ila ta gina, wadda ta raba yankunansu da ke yammacin kogin Jordan da kuma birnin Qods, da ke nuna goyon bayansu ga Amurkawa da ke zanga-zangar adawa da siyasar nuna wariya.

Daga cikin abubuwan da suka zana har da hotunan George Floyd bakar fata da ‘yan sanda farar fata suka kashe a Amurka makonni biyu da suka gabata, wanda ya yi sanadiyyar barkewar zanga-zanga a fadin kasar, kamar yadda kuma aka yi rubuce-rubuce a kan katangar na nuna adawa da siyasar zalunci da nuna fin karfi a kan raunana a ko’ina cikin fadin duniya.

Daya daga cikin wadanda suka yi zane-zanen mai suna Taqiyuddin Sabatin ya bayyana cewa, manufarsu ta yin hakan ita ce nuna wa duniya cewa suna tare da dukkanin wadanda ake zalunta a duniya, duk kuwa da cewa su ma suna karkashin irin wannan zaluncin tsawon shekaru.

Ya cea akn haka ne ma suka zabi su yi wannan zane a kan katangar wariya da Isra’ila ta gina a cikin yankunan Falastinawa.

 

3904080

 
 

 

 

 

 

captcha