IQNA

Kungiyar Nujba Ta Jaddada Wajabcin Ficewar Dakarun Amurka Daga Iraki

23:54 - June 21, 2020
Lambar Labari: 3484914
Tehran (IQNA) kungiyar dakarun Nujba a kasar Iraki ta bukacia aiawatar da kudirin majasar dokokin kasar kan ficewar sojojin Amurka daga Iraki.

A wata sanarwa da kungiyar ta “Harkatun-Nujabaa” ta fitar a jiya Asabar ta jadadda wajabcin aiwatar da kudurin da ya fito daga Majalisar dokokin kasar ta Iraki wanda ya bukaci ficewar dukkanin sojojin kasashen waje daga kasar.

Bugu da kari shugaban kungiyar, Mustafa al-Kazimy ya yi kira da a dauki mataki mai karfi na takawa kasar Turkiya birki akan kutsen da ta ke yi cikin Iraki da kare kasar daga mamayarta.

Har ila yau shugaban kungiyar ta “Harkatun-Nujaba’ah” ya bayyana mamakinsa akan yadda Amurka ta ke tsoma baki a harkokin cikin gidan Iraqi ta hanyar batun wanda yake da hakkin rike makami.

3905864

 

 

captcha