IQNA

Hamas Ta Soki Laraban Da Ke Hankoron Kulla Aalaka da Isra'ila 

17:48 - June 26, 2020
Lambar Labari: 3484929
Tehran (IQNA) Kunginyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas ta bayyana cewa, kasashen larabawan da suke zaton za su samu tsaro ta hanyar kulla alaka da Isra’ila suna tafka babban kure.

Tashar alalam ta bayar da rahoton cewa, shugaban ofishin alaka ta kasa da kasa na kungiyar Hamas Dr. Musa Abu Marzuk ya bayyana cewa, babu wata hanya da al’ummar Falastinu za su samu ‘yancin kansu sai ta hanyar gwagwarmayar kalubalantar ‘yan mamaya.

Musa Abu marzuk ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da kafar yada labarai ta Al-sabil, inda ya jaddada cewa al’ummar Falastinu ba za su taba canja matsayinsu na neman hakkokinsu da aka haramta musu a cikin kasarsu ba.

Haka nan kuma ya bayyana kasashen larabawan da suke ta hankoron ganin sun samu kusanci da Isra’ila tare da kulla a alaka da ita domin neman yardarm Amurka, ko kuma da sunan neman samun hanyoyin tabbatar da tsaron kasashensu, ya ce wadannan kasashe suna tafka babban kure.

Ya ce wannan babban abin ban takaici, ta yadda kasashe da gwamnatocin da ya kamata su zama a sahun gaba wajen kare hakkokin al’ummar Falastinu, maimakon haka sai suka zama a sahun gaba wajen hada kai da makiya al’ummar Falastinu domin cutar Falastinawa.

 

3906972

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: sahun gaba ، ya kamata ، hankoron ganin ، kasashen larabawan ، kusanci ، zantawa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :