IQNA

Martanin Iran Kan Batun Yarjejeniyar Kasuwanci Ta Shekaru Tsakaninta Da China

23:32 - July 08, 2020
Lambar Labari: 3484964
Tehran (IQNA) Sayyid Abbas Musawi kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya mayar da martani dangane furucin jami’an Amurka kan yarjejeniyar kasuwanci ta shekaru 25 tsakanin Iran da China.

Shafin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayar da rahoton cewa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Musawi ya fitar da bayani da ke mayar da martani kan yadda jami’an gwamnatin Amurka suka fusata da batun yarjejeniyar kasuwanci tsakanin China da Iran.

Musawi ya ce a ziyarar da shugaba Rauhani ya kai kasar China da wadda shugaba Jinping na China ya kawo Iran ne aka cimma wannan yarjejeniya, kuma har yanzu ana ci gaba da tatatuna hanyoyin aiwatar da ita.

Ya ce kalaman da suke fitowa daga bakunan jami’an wasu kasashe da ke kiyayya da Iran da China, ba komai ba ne illa yanke kauna daga fatan da suke da ita, na ganin sun durkusar da kasashen biyu.

Musawi ya kara da cewa, aiwatar da wannan yarjejeniyar amfanin al’ummomin dukkanin kasashen biyu ne, kuma da zaran an kammala yin bita kan batun za a mika shi ga majalisa domin yin dubi, kafin fara aiwatar da yarjejeniyar.

Haka nan kuma ya yi ishara da batun da ake yi kan cewa China ta karbi hayar wasu tsibiran Iran guda biyu a cikin tekun fasha da cewa wannan maganar ba ta da tushe balantana asali.

3909478

 

Abubuwan Da Ya Shafa:
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha