IQNA

Red Cross: Kashi 66 Na Mutanen Yemen Suna Bukatar Taimakon Abinci

19:11 - July 12, 2020
Lambar Labari: 3484977
Kungiyar bayar da agaji ta Red Cross ta bayyana cewa fiye da rabin mutanen Yemen suna bukatar taimakon abinci.

Kamfanin dillancin labaran sputnik ya bayar da rahoton cewa, kungiyar bayar da agaji ta kasa da kasa red cross ta bayar da wani rahoto da ke nuni da cewa kashi 66 na mutanen Yemen ba su da abincin da za su ci,  yayin da 11 cikin dari kuma suna samun abinci maras kyau.

Sai kuma kashi 64 ba su da hanyoyin da za su iya samun taimako na likita ko kuma maguna da suke bukata saboda rashin lafiya, yayin da kashi 58 ba su iya samun ruwan sha mai tsafta.

Yawan muaten kasar Yemen dai ya kai kimanin miliyan 30, amma shekaru 5 kenan a jere da gwamnatin Saudiyya take yin luguden wuta a kansu, wanda hakan ne ya jefa su a cikin wannan mawuyacin halain.

 

3909972

 

 

captcha