IQNA

Manufa Da Tsayin Daka A Kanta Su Ne Muhimman Darussan Ashura

23:20 - August 29, 2020
Lambar Labari: 3485130
Tehran (IQNA) shugaba n cibiyar musulunci ta birnin Jakarat Indonesia ya bayyana cewa, manufa da tsayin daka akanta su ne muhimman darussan ashura.

Hojjatol Islam Abdulmajid Hakim Ilahi shugaba n cibiyar musulunci ta birnin Jakarat Indonesia ya bayyana cewa, manufa da tsayin daka akanta su ne muhimman darussan wannan harka ta Imam Hussain ke koyar da mu.

A irin wannan rana dai miliyoyin al’ummar musulmi musamman mabiya tafarkin Ahlulbaiti (a.s) ne a duk faɗin duniya ne suka gudanar da juyayin ranar Tasu’a, wato ranar 9 ga watan Muharram, kwana guda kafin juyayin ranar Ashura, ranar da aka kashe Imam Husain, jikan Annabi (a.s) tare da mabiyansa a Karbala.

Ita dai wannan rana ta Tasu’a, wacce aka fi saninta da ranar Biyayya Da Tsayin Daka – an ware ta ne don tunawa da irin gagarumar sadaukarwar da Abbas Ibn Ali, dan Imam Ali (a.s) kana kuma kani ga Imam Husaini (a.s) yayin abin da ya faru a Karbala ɗin.

An kashe shi ne a ƙoƙarinsa na kawo ruwa ga mata da ƙananan yara da suke sansanin Imam Husaini (a.s) bayan da aka hana su ruwa na kwanaki, inda maƙiya suka masa ƙawanya da kuma kashe shi.

A kowace irin wannan ranar dai masu zaman makoki da juyayi su kan taru a masallatai da Husainiyoyi don nuna alhini da kuma juyayin su ga abin da ya faru ga Iyalan Annabi (s.a.w.a) a Karbala.

3919493

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: masallatai tarukan addini
captcha