IQNA

Sayyid Nasrullah:

An Sha Yi Mana Tayin Makudan Kudade Domin Mu Bar Fada Da Zalunci Da Mamayar Isra'ila

21:24 - August 30, 2020
Lambar Labari: 3485134
Tehran (IQNA) Babban sakataren kungiyar Hizbullah ya bayyana cewa, Amurka ta sha yi wa kungiyar tayin makudan kudade domin ta daina adawa Isra’ila ta kuma daina taimakon Falastinawa.

Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa, Amurka ta sha yi wa kungiyar Hizbullah tayin makudan kudade, da kuma mika mata mulki a Lebanon, amma bisa sharadin cewa ta daina adawa Isra’ila ta kuma daina taimakon Falastinawa da ake zalunta.

A lokacin da yake gabatar da jawabi a daren jiya Asabar a taron daren Ashura, babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa, tun daga shekara ta 2000, Amurka ta sha yi wa kungiyar Hizbullah tayin makudan kudade, da kuma mayar da siyasar Lebanon daidai da abin da Hizbullah ke so wajen tafiyar da mulkin kasar, bisa sharadin cewa Hizbullah ta daina adawa Isra’ila ta kuma daina taimakon Falastinawa da sauran raunana, amma Hizbullah ba ta taba amincewa da haka ba.

Ya ce babu yadda za a yi kungiyar Hizbullah ta zama ‘yar ba ruwanmu a batun yaki tsakanin gaskiya da bata, kungiyar ta dauka wa kanta cewa dole ne ta kasance tare da gaskiya a duk inda take domin yaki da karya da bata da zalunci, tare da kasancewa da raunana wadanda aka zalunta.

Dangane da yadda kafofin yada labarai na bangarorin da ke kiyayya da kungiyar suke ci gaba da yin dirar mikiya a kankungiyar kuwa, Sayyid Nasrullah ya bayyana cewa; ba a taba samun wani lokaci wanda kungiyar take fuskantar zalunci da karairayi daga kafofin yada labarai na bangarori da gwamnatoci masu kiyayya da ita kamar wannan lokaci ba.

Ya ce duk wannan ba zai taba sanya kungiyar ta canja matsayinta na kasacewa tare da gaskiya ba a duk inda take.

 

3919842

 

captcha