
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Said Khatib Zadeh ya bayyana cewa, taron da shugabannin kungiyoyin Falastinawa suka gudanar, ya tabbatar da irin hikima da kaifin basira ta al’ummar Falastinu, wadanda suka tsaya kan neman ‘yanci daga mamayar yahudawan Isra’ila.
Ya ci gaba da cewa, wannan taro da kuma abin day a cimmawa, ya kara tabbatar da cewa al’ummar Falastinu tan anan kan bakanta na kin mika wuya ga manufofin yahudawa ‘yan mamaya, ko da kuwa wasu daga cikin larabawa masu cin amana sun mika wuya ga manufofin yahudawa.
Khatib Zadeh ya ce duk da irin matsaloli da al’ummar Falastinu suka fuskanta tsawon shekaru da mamaye kasarsu da yahudawan sahyuniya suka yi, amma sun ci gaba da yin juriya da kuma yin gwagwarmayar neman kwatar ‘yancin kansu, wanda kuma ko badade ko bajima, da yardar Allah nasara tana tare da su.
3921039