IQNA

Hainiyya Ya Bkaci A Kafa Gwamnatin Hadin Kan Kasa Ta Falastinu

22:40 - September 07, 2020
Lambar Labari: 3485158
Tehran (IQNA) shugaban kungiyar Hamas Isma’il haniyya ya bayyana cewa kafa gwamnatin hadin kan kasa shi ne babban abin da zai rarrabuwa tsakanin Falastinawa.

Shafin yada labarai na Falastine ya bayar da rahoton cewa, a wata zantawa ta talabijin a birnin Beirut,  shugaban kungiyar Hamas Isma’il haniyya ya bayyana cewa kafa gwamnatin hadin kan kasa shi ne babban abin da zai rarrabuwa tsakanin Falastinawa baki daya.

Haniyya ya ce daga cikin abin da ya kamata a yi hard a gudanar da zabuka na ‘yan majalisa a dukkanin bangarori na yammacin kogin Jordan da kuma zirin gaza da gabashin Quds.

Bayan nan kuma aka kafa gwamnati wadda za ta hada dukkanin bangarori na al’ummar falastinu, wanda hakan shi ne zai kawo hadin kai da kuma yin magana guda daya da sunan dukkanin al’ummar falastinu.

Haniya ya ce yin hakan zai kawo karshen killace yankin zirin Gaza da Isra’ila ke yi, kamar yadda hakan kuma zai bai wa Falastinawa damar yin magana da yawu daya  a duniya, wanda shi ne abin da Isra’ila take tsoro.

3921513

 

captcha