IQNA

22:44 - September 07, 2020
Lambar Labari: 3485160
Tehran (IQNA) wata yariyar ‘yar shekaru 4 da haihuwa mai ilimin lissafi kuma mahardaciyar kur’ani

Shafin yada labarai na sadal Balad ya bayar da rahoton cewa, a jiya tashar talabijin ta alhayat ta gayyaci yarinyar mai suna Nur Makki a wani shiri, inda aka yi mata tambayoyi masu matukar ahala dangane da lissafi, da kuma wasu ayoyi na kur’ani amma duk ta amsa su.

Daga cikin tambayoyin da aka yi mata a kan lissafi har da wadanda suke da sarkakiya matuka, amma kuma abin da ya baiwa kowa mamaki yadda ta amsa su daidai, kamar yadda kuma aka yi mata tambayoyi kan ayoyin kur’ani tana bayar da amsa tare da bayanin surorin da ayoyin suke ciki.

Ibrahim Makki shi ne kawon yarinyar, wanda ya bayyana cewa lamarin yarinyar wani ikon Allah ne kawai wanda shi kadai ya san ajiyar da ya yi.

 

3921406

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: