IQNA

Martanin Al'ummar Falastinu Kan Sarakunan Larabawa Da Ke Cin Aamanarsu

21:27 - September 16, 2020
Lambar Labari: 3485193
Tehran (IQNA) Falastinawa sun ce babu batun zaman lafiya a gabas ta tsakiya matukar ba a kawo karshen mamayar Isra’ila a kan kasar Falastinu ba.

Falastinawa sun bayyana cewa, babu batun zaman lafiya a gabas ta tsakiya, matukar ba a kawo karshen mamayar da Isra’ila take yi a kan kasar Falastinu da kuma zalunci da kisan kiyashin da take yi a kan al’ummar Falastinu ba.

امضای توافق سازش بحرین و امارات با رژیم صهیونیستی/ تظاهرات هزاران فلسطینی در کرانه باختری

A lokaci da yake mayar da martani dangane da yarjejeniyar da aka kulla tsakanin wasu kasashen larabawa da Isra’ila da aka kira ta zaman lafiya, Shugaban Falastinawa ya bayyana cewa, batun kulla yarjejeniyar zaman lafiya wasu da ba su da wata matsala da Isra’ila tamkar wasan kwaikwayo ne.

Ya ce al’ummar falastinu su ne suke da matsala da Isra’ila, domin kuwa ta mamaye musu kasa, ta mayar da ita kasar yahudawa ‘yan share wuri zauna da suka zo daga wasu kasashen duniya, a lokaci guda kuma ta kori miliyoyin Falastinawa daga kasarsu sun zama ‘yan gudun hijira a wasu kasashe, sauran da suka rage kuma tana kashe su tare da ci gaba da rushe musu gidaje, ya ce zaman lafiya shi ne kawo wannan ta’adi na Isra’ila.

امضای توافق سازش بحرین و امارات با رژیم صهیونیستی/ تظاهرات هزاران فلسطینی در کرانه باختری

Dubban Falastinawa ne suka gudanar da zanga-zanga a cikin biranan yankin yammacin kogin Jordan da kuma zirin Gaza gami da birnin Quds, domin yin tir da Allawadai da larabawan da suka mika wuya ga yahudawa, domin cutar da al’ummar Falastinu.

امضای توافق سازش بحرین و امارات با رژیم صهیونیستی/ تظاهرات هزاران فلسطینی در کرانه باختری

Al’ummomin larabawa da na musulmi a kasashe daban-daban suna ci gaba da yin tir da Allawadai da wannan mataki, wanda suke kallonsa a matsayin cin amana ga al’ummar Falstinu da ma sauran larabawa da musulmi.

3923210

 

 

captcha