IQNA

An Bayar Da Kyautar GIFA Ta Duniya Ta 2020 Ga Jaiz Bank Na Najeriya

22:39 - September 22, 2020
Lambar Labari: 3485207
Tehran (IQNA) an bayar da babbar kyautar shekara-shekara ta tsarin harkokin kudade a musulunci ta duniya wato GIFA ga bankin Jaiz na Najeriya.

Jaridar The Sun ta bayar da rahoton cewa, Jaiz Bank Plc na Najeriya, ya karbi kyautar shekara-shekara ta tsarin harkokin kudade a musulunci ta duniya wato (Global Islamic Finance Awards) GIFA a takaice ta wanann shekara  ta 2020.

Kyautar GIFA na daga cikin manyan kyautuka na bankin musulunci a duniya, wadda gwamnatin kasar Malaysia ce ta assasa wannan tsari na bayar da wannan kyauta a kowace sheakara.

Bisa ga sanarwar da kwamitin GIFA ya bayar, bankin Jaiz a Najeriya, ya cancanci wannan kyauta a wanna shekara, bisa la’akari da hidimar da ya gudanar a bangarori daban-daban, ta fuskancin kiyaye ka’idoji na musulunci a mu’amalar kudade, da kuma yin aiki da dukkanin alkawullansa ga jama’a.

Hassan Usman babban manajan daraktan bankin da ked a babban ofishinsa a Abuja, ya bayyana cewa wannan babban abin farin ciki ne a gare su, kuma hakan zai kara karfafa gwiwarsu wajen ci gaba da kara bayar da himma domin gudanar da aikinsu a bisa ka’idojin da suke bi a cikin nasu.

 

3924590

 

 

 

 

 

 

captcha