IQNA

Masu Kiyayya da Musulunci Sun sake Keta Alfarmar Kur’ani Mai Tsarki

22:44 - October 04, 2020
Lambar Labari: 3485243
Tehran (IQNA) masu tsananin kiyayya da addinin muslunci a kasar Denmark sun sake keta alfarmar kur’ani mai tsarki.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, ‘yan jam’iyyar Stram Kurs masu tsanin kiyayya da addinin muslunci sun yi gangami a garin Fardrishia, wanda akasarin mazauna yankin musulmi da suka yi hijira daga Turkiya da wasu kasashen musulmi, inda suka kona kwafin kur’ani mai tsarki.

Wannan lamari dai ya bakanta ran jama’a da dama da suke yankin, inda suka nuna fushinsu da rashin yarda kan wannan danyen aiki, inda jami’an ‘yan sanda suka kama wasu.

Mutanen da suka yi wannan batunci da cin zarafi ga addinin muslunci dai ‘ya’yan wata jam’iyyar siyasa ce da aka kafa mai tsatsauran ra’ayin kin jinin addinin muslunci a kasar, kuma jam’iyyar tana da wakilci a majalisar dokokin kasar.

Dukkanin abubuwan da ‘ya’yan wannan jam’iyya suke aikatawa na keta alfarmar abubuwa masu tsarki a  cikin addinin muslucni, yana a matsayin bayyana ra’ayi ne a mahangar gwamnatin kasar ta Denmark.

3927140

 

 

captcha