IQNA

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci A Iran:
22:12 - November 03, 2020
Lambar Labari: 3485331
Tehran (IQNA) Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar Iran ba ta damu kan waye zai lashe zaben shugabancin Amurka ba

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar Iran ba ta damu kan waye zai lashe zaben shugabancin Amurka ba sannan kuma matsayar Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan siyasar mulkin mallakar Amurka tana nan daram ko ma waye ya lashe zaben Amurkan.

Jagoran ya bayyana hakan ne a yayin da ya ke gabatar da jawabin ranar maulidin Annabi Muhammadu (s.a.w.a) da kuma jikansa Imam Sadiq (a.s) kana kuma a ranar karshe na Makon Hadin Kai wanda aka watsa kai tsaye ta gidan talabijin din kasar Iran inda ya ce: Siyasar Iran dangane da Amurka, wata tsararriyar siyasa ce wacce kuma take a fili, don haka ba ta sauyawa don kawai an sami sanyin wani mutum.

Imam Khamenei ya ci gaba da cewa: Wasu suna tunanin cewa wata gwamnati za ta amfana sakamakon mika kai ga bukatun Amurka, alhali kuwa gwamnatocin da suka mika kai ga mulkin mallakar Amurka sun fi cituwa nesa ba kusa ba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce babban dalilin kiyayyar da Amurka take yi da Iran da gwamnatin Musulunci ta kasar shi ne kin mika kai da Iran ta yi ga bakar siyasar Amurkan. Don haka sai ya ce wannan kiyayyar kuwa za ta ci gaba, sannan hanya guda ta kawo karshenta shi ne lokacin da Amurkan ta yanke kaunar cewa za ta iya cutar da al’ummar Iran.

Yayin da ya ke magana kan batancin da aka yi wa Manzon Allah (s.a.w.a) a kasar Faransa da kuma nuna goyon bayan hakan da gwamnatin kasar ta yi kuwa, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi kakkausar suka ga wannan matsaya ta gwamnatin Faransa da kuma shugaban kasar.

Jagoran ya bayyana abin da ke faruwa a kasar Faransan a matsayin bayyanar da siyasar kiyayya da Musulunci da ma’abota girman kan duniya da kuma sahyoniyawan duniya suke aiwatarwa ba wai kawai wani kuskure ne wanda wani mai zane yayi ba.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Maimakon a dauki wannan lamari a matsayin wani kuskure da wani mai zane yayi, lalle lamarin ya wuce nan. Lamarin yana nuni da cewa lalle akwai wasu boyayyun hannaye cikin lamarin.

Imam Khamenei ya jijinawa irin yadda al’ummar musulmi suka fito suka nuna fushi da kuma rashin yardarsu da wannan danyen aikin yana mai cewa hakan yana nuni da cewa al’ummar musulmi a farke suke.

Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi watsi da fakewar da gwamnatin Faransa ta yi wajen goyon bayan zanen batancin da aka yi wa Annabi (s.a.w.a) da cewa ta yi hakan ne saboda ‘yancin fadin albarkacin baki da kuma kare hakkokin bil’adama, yana mai cewa gwamnatin Faransar da take fadin wannan magana ita ce kuma gwamnatin da ta ke ci gaba da ba da mafaka ga ‘yan kungiyar munafukai ta MKO ‘yan ta’adda wadanda suka dubun dubatan al’ummar Iran.

Imam Khamenei ya ci gaba da cewa: Lalle akwai darasi cikin wannan lamarin. Gwamnatin Faransan da take magana kan kare hakkokin bil’adama da ‘yancin fadin albarkacin baki, ita ce dai kuma gwamnatin da take ci gaba da goyon bayan mafiya munin kungiyoyin ‘yan ta’adda a duniya wadanda suka kashe shugaban kasar Iran, alkalin alkalai, firayi minista da sauran jami’an kasar Iran bugu da kari kan sama da Iraniyawa 17,000.

Tun da fari dai sai da Jagoran yayi magana kan muhimmancin hadin kai tsakanin al’ummar Musulmi da kuma jinjinawa hangen nesar marigayi Imam Khumaini (r.a) na sanya wa wadannan ranaku na haihuwar Ma’aikin Allah (s.a.w.a) a matsayin ranakun makon hadin kai, yana mai cewa abubuwan da suke faruwa a halin yanzu a duniyar musulmi suna kara nuni da wajibcin hadin kai da kuma kara tabbatar da hakan a tsakanin al’ummar musulmi.

Har ila yau kuma a wani bangare na jawabin nasa Ayatullah Sayyid Ali Khamenei yayi ishara da ha’inci da cin amanar da wasu kasashen larabawa suka yi na kulla alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila inda yayi Allah wadai da hakan, sai dai kuma ya ce: Tabbas hakan ba zai kawo karshen lamarin Palastinu ne. Kasar Palastinu dai ta Palastinawa ce, kuma ko shakka babu za a kawo karshen Sahyoniyawa ‘yan share guri zauna.

 

 

3933049

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: