IQNA

Martanin Hizbullah Kan Tsoma Bakin Amurka A Siyasar Lebanon

23:45 - November 07, 2020
Lambar Labari: 3485345
Tehran (IQNA) kungiyar Hizbullah ta zargi Amurka da yin shigar shigula a cikin harkokin kasar Lebanon na cikin gida.

Kungiyar gwagwarmayar ta kasar Lebanon ta ba bayyana cewa takunkumin da a Amurka ta kakaba wa shugaban jam’iyyar “Tayyarul Watdi al-Hur” tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar.

A wani bayani da kungiyar ta Hizbullah ta fitar da marecen jiya Juma’a ta ce; Amurka ita ce babbar mai renon ‘yan ta’adda da tsattsaurin ra’ayi a duniya, haka nan kuma ita ce mai kare gwamnatocin kama-karya wadanda su ke gurbatattun, don haka ba ta da bakin fada akan fada da cin hanci da rashawa a duniya.

A jiya Juma’a ne dai babban baitul-malin Amurka ya sanar da kakaba wa shugaban jam’iyyar “Tayyar Watdiyul-Hur, na Lebanon, Jubran Basil. Takunkumi.

Bayanin na Hizbullah ya ci gaba da cewa; Amurka tana amfani da dokokinta na cikin gida da suka kunshi wadanda take kira na fada da ta’addanci, domin shimfida ikonta a duniya baki daya. Tana kuma yin amfani da wadannan dokokin ne akan duk wata kasa ko wani mahaluki mai ‘yanci da bai mika wuya ga manufofinra.

Kungiyar ta Hizbullah ta ce; Tana tare da kungiyar “Tayyarul-Wadhniyyil-Hur” da shugabanta, sannan kuma ba ta amince da wannan takunkumin na zalunci ba.

 

3933545

 

 

captcha