IQNA

Cibiyar Azhar Ta Yaba Da Matakin da Kasashen Turai Suka Dauka Kan Mai Kiyayya da Muslunci

22:38 - November 14, 2020
Lambar Labari: 3485367
Tehran (IQNA) cibiyar Azhar ta yaba da irin matakin da kasashen turai suka dauka na korar Rasmus Paludan daga cikin kasashensu.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, babbar cibiyar addini ta Azhar dake kasar masar ta fitar da bayani, wanda a cikinsa ta yaba da irin matakin da wasu daga cikin kasahen turai suka dauka na hana Paladan gudanar da gangamin kona kur’ani.

Bayanin ya ce matakin da kasashen Faransa da Belgium suka dauka na cafke Rasmus Paladan tare da hana shi gudanar da gangamin kona kur’ani tare da mutaensa, wannan babban abin yabawa ne.

Cibiyar Azhar ta ce irin abin da Paludan ke yin a nuna tsananin kiyayya da muslumi da kuma addinin muslunci, yana daga cikin abubuwan da suke kawo rashin zaman lafiya a tsakanin mabiya addinai, kuma abin da yake aiwatarwa baya wakilatar mabiya addinin kiristanci, domin kuwa kiristoci ba makiyan musulmi ba ne, kamar yadda musulmi ba makiyan kiristoci ba ne.

 

3934992

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha