IQNA

Zarif Ya Jaddada Wajabcin Janye Takunkuman Zalunci Da Aka kakaba Wa Syria

22:34 - November 23, 2020
Lambar Labari: 3485393
Tehran (IQNA) Muhammad Jawad Zarif Ministan harkokin wajen Iran ya bukaci ganin an daukewa kasar ta Syria dukkanin takunkuman da aka dora a kanta.

Ministan harkokin wajen Iran Muhammad Jawad Zarif wanda ya gana da manzon musamman na MDD zuwa kasar Syria,Geir Otto Pedersen a yau Lahdi, ya bukaci ganin an daukewa kasar ta Syria dukkanin takunkuman da aka kakaba ma ta.

Muhammad Jawad Zarif ya kuma bayyana takunkumin da aka kakaba wa gwamnati da al’ummar Syria da cewa na zalunci ne, musamman a cikin wannan yanayin na annobar corona.

Muhammad Jawad Zarfi ya kuma yi ishara da yadda wasu kasashe su ke son ganin matsaloli a kasar Syria sun ci gaba, sannan ya kara da cewa: A shekarar da ta gabata an sami damammaki na dagewa kasar Syria takunkuman da aka kakaba ma ta, amma mun ga yadda wasu kasashen su ka yi wa shirin kafar angulu.

A nashi gefen, manzon musamman na MDD a kasar Syria ya yi bayani akan kokarin da yake yi domin ganin an yi taro na gaba akan Syria, da kuma na kwamitin rubuta tsarin mulki.

3936701

 

 

captcha