IQNA

China Na Daukar Matakan Rusa Alamomi Na Muslucni ta Hanyar sauya Wa Masallatai Fasali

22:57 - November 25, 2020
Lambar Labari: 3485398
Tehran (IQNA) gwamnatin kasar China tana daukar matakai na rusa wasu alamomi da ke nuni da addinin musulunci daga ciki hard a sauya fasalin masallatai na musulmi.

Rahotanni sun tababtar da cewa, mahukuntan kasar China da sunan yin gyara a masallacin Nangwan da ke yankin Ninxia, sun sauya fasalin masallacin, tare da rusa tulluwa da kuma hasumomiyin masallacin.

Bayanin ya ce irin wannan mataki yana nufin kawar da alamu na addinin muslunci, domin kuwa yaayin ginin masallatai yana nuni ne da yanayi na muslunci da kuma tsoffin al’adunsa.

Haka nan kuma gwamnatin kasar ta China ta sanya doka kan a daina gina masallatai masu tulluwa ko kuma hasumiya a wannan yanki wanda akasarin wadanda suke ynakin msuulmi ne.

 

 

 

3937231

 

 

 

 

 

 

captcha