IQNA

Hadaddiyar Daular Larabawa Ta Haramta Wa Wasu Kasashen Musulmi Shiga Kasarta

21:43 - November 26, 2020
Lambar Labari: 3485403
Tehran (IQNA) Gwamnatin hadaddiyar daular larabawa ta dauki mataki hana bayar da izinin shiga cikin kasarta ga kasashe 13 da suka hada da na larabawa da na musulmi.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, gwamnatin kasar hadaddiyar daular larabawa ta dauki mataki hana bayar da izinin shiga cikin kasarta ga kasashe 13, da suka hada da na larabawa da kuma na musulmi, daga ciki har da Iran, Pakistan da kuma Afghanistan gami da Turkiya da Kenya.

Daga cikin kasashen larabawa kuwa akwai Iraki, Aljeriya, Libya, Syria, Tunisia, Yemen da kuma Lebanon, wanda kuma gwamnatin UAE ta dauki wanna mataki tun daga ranar 18 ga wannan wata na Nuwamba da muke ciki.

Mahkuntan kasar ta hadaddiyar daular larabawa wato UAE, ba ta bayyana dalilin daukar wanann mataki ba, ta dai bayyana cewa bayar da izinin shiga ‘yan wadannan kasashe yana tattare da hadari.

To sai dai wasu na danganta hakan ne da batun kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila da kasar UAE ta yi, inda suke danganta hakan da batun tsaro ga yahudawa a cikin kasar.

Gwamnatin UAE ta haramta bayar da iznin shiga kasarta ga wadannan kasashen muslmi da na larabawa ne, a daidai lokacin da ta bayar da izinin shiga cikin kasarta ga yahudawan Isra’ila ba tare da visa ba.

 

3937389

 

 

 

captcha