IQNA

Taron OIC A Nijar Ya Yi Dubi Kan Yaki Da Ta’addanci Da Taimakon Al’ummar Falastinu

22:15 - November 28, 2020
Lambar Labari: 3485409
Tehran (IQNA) taron OIC a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar ya mayar da hankali batun yaki da ta’addanci.

Taron ministocin harkokin wajen kasashen musulmi na kungiyar OIC a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar, ya mayar da hankali batun yaki da ta’addanci, da kuma nuna kyamar musulmi a wasu kasashen duniya, da sauran matsaloli da suke ci wa musulmi tuwo a kwarya.

Taron wanda aka bude a jiya a birnin Yamai fadar mulkin jamhuriyar Nijar, ya samu halartar ministocin harkokin waje da tawagogi na kasashe 57, inda aka tattauna batutuwa da suke da alaka da yaki da ta’addanci, da kuma batun nuna kyama da ake a kan musulmi musamman a wasu kasashen turai.

A lokacin da yake gabatar da jawabin bude zaman taron na OIC karo na 47 a jiya, Shugaban Jamhuriyar Nijar Muhammadu Issofou ya bayyana cewar, kashi 82 na al’ummar duniya da hareiharen ta’addanci ke rutsawa da su Musulmi ne, yayin da kasashen Musulmi ke kashe makudan kudade daga kasafin kudinsu wajen yaki da ta’addanci.

Ya ce lokaci ya yi da kasashen Musulmi za su hada kan su, musamman wadanda ke Yankin Sahel wajen shawo kan matsalar ayyukan ta’addancin da ya addabe su, kamar yadda kuma ya ce, ya dace a dinga samu musayar bayanan asiri a bangaren soji da kuma aiki tare wajen shawo kan wannan matsala.

Yusuf Al-usaimin babban sakataren kungiyar ta OIC ya fadi a wajen taron cewa, ta’addanci shi ne babbar barazana ga dukkanin al’ummomin musulmi, kuma ya zama wajibi a mike domin yakar sa, ta dukkanin hanyoyi da suka dace.

A nasa bangaren ministan harkokin wajen kasar Turkiya Jawish Auglo a cikin jawabin da ya gabatar ya bayyana cewa; wani abu da yake da muhimamnci a mayar da hankali akansa shi ne batun karuwar kyamar addinin muslucni a cikin kasashen turai, inda wasu daga cikin shugabanni turai suke kokarin yin gyara a kan addinin muslunci, inda suke kiransa da addinin ta’addanci.

 

3937741

 

captcha