IQNA

Cibiyoyin Musulmi A Uganda Sun Yi Alawadai Da Kisan Masanin Nukiliya Dan Kasar Iran

23:44 - November 30, 2020
Lambar Labari: 3485414
Tehran (IQNA) cibiyoyin musulmi a kasar Uganda sun yi tir da Allawadai da kisan da aka yi wa masanin ilimin nukiliya dan kasar Iran.

Cibiyoyin musulmi a kasar Uganda sun bayyana kisan da aka yi wa masanin ilimin nukiliya dan kasar Iran da cewa abin Allawadai ne kuma laifi ne ya cancanci a hukunta masu hannu a cikinsa.

A cikin bayanai daban-daban da kngiyoyin musulmi na kasar Uganda suka fitar, sun bayyana kisan babban masanin ilimin nukiliya na kasar Iran farfesa Mohsen Fakhrizadeh da cewa, manufar hakan ita ce raunana musulmi ba Iran kawai ba.

Daga cikin bangarorin da suka fitar da bayai akwai babbar ibiyar kur'ani ta kasar Uganda ta Kur'an wa Itra, baya ga haka kuma akwai makarantu na naarin addini, wadanda duk sun aike da sakonnin ta'aziyya da alhini zuwa ga ofishin jakadancin kasar Iran da ke kasar.

Kungiyoyi da cibiyoyin musuluni a kasar Uganda suna da kyakkyawar alaka da kasar Iran, kamar yadda kuma sukan shirya taruka da suke hada dukkanin bangarorin musulmi da suke da fahimta daban-daban.

Musulmin Uganda suna zaman lafiya tare da dukkanin sauran mabiya addinai a kasar, inda suke girmama fahimtar juna.

 

3938215 

 

 

 

captcha