IQNA

Wata Tawagar Gwamantin Bahrain Ta Ziyarci Masallacin Quds A Asirce

23:50 - November 30, 2020
Lambar Labari: 3485415
Tehran (IQNA) wata tawagar jami'an gwamnatin Bahrain ta ziyarci masallacin Quds karkashin kulawar yahudawan Isra'ila a asirce.

Jaridar Ra'ayul yaum ta bayar da rahoton cewa, wata tawagar jami'an gwamnatin Bahrain ta ziyarci masallacin Quds karkashin kulawar yahudawan Isra'ila a asirce, karkashin Jagorancin Khalin Bin Khalifa Al Khalifah dan uwan sarkin kasar ta Bahrain.

A wata zantawa da ta hada da shi da gidan rediyon Isra'ila a jiya, Khalin Bin Khalifa ya bayyana cewa, lalai sun ziyarci masallacin Quds, kuma jami'an tsaro Isra'ila ne suka ba su kariya.

Ya bayyana cewa a ziyarar tasu wadda ba a bayyana ba, sun gana da manyan jami'an Isra'ila, kuma sun cimma yarjejeniya a akn abubuwa daban-daban na bunkasa alaka tsakanin Isra'ila da masarautar Bahrain.

Wanann dai na zuwa ne a karkashin shirin shugaban Amurka mai barin gado, wanda ya yi amfani da kasashen larabawa 'yan amshin shatan Amuka wajen tilasta su da su kulla alaka da gwamnatin yahudawa Isra'ila, domin sama ma Isra'ila halasci, inda Barain da UAE suka fara kulla wannan laka, kafin daga bisani Sudan ta bi sahunsu.

 

 

3938238

 

 

 

captcha