IQNA

Cibiyar Hubbaren Abbas Za Ta Samar Da Manhajar Kur’ani Ta Hanyar Wayar Salula

22:44 - December 01, 2020
Lambar Labari: 3485418
Tehran (IQNA) cibiyar  hubbaren Abul Fadl Abbas za ta samar da manhajar koyoyon ilmomin kur’ani mai tsarki ta hanyoyin wayar salula .

Tashar talabijin ta Alkafil ta bayar da rahoton cewa, bangaren kula da ayyukan kur’ani na cibiyar  hubbaren Abul Fadl Abbas zai samar da manhajar koyoyon ilmomin kur’ani mai tsarki ta hanyoyin wayar salula, wanda za a iya yin amfani da su cikin sauki.

Wannan tsari na manhajar kur’ani zai kunshi cikakken kur’ani mai tsarki, da kuma nau’oin kira’a daga fitattun makaranta kur’ani na duniya, kamar yadda kuma zai iya bayar da tsari na koyoyon karatu ko tajwidi.

Haka nan kuma tsarin manhajar yana yi ma mutum gyara idan ya yi kure wajen karatun kur’ani, kamar yadda kuma yana bayar da bayanai na tafsirin ayoyi da kuma bayanai na hukunce-hukunce da suke cikin ayoyin kur’ani, wanda duk yana cikin tsarin manhajar.

Akwai wasu abubuwa na daban da suka hada da:

  . Saukar Kur’ani a bangaren ma da kuam bangaren maza

  . Tsarin gyaran karatun kur’ani da fitar da ilmomin da ke cikin ayoyi

  . Mutane 150 za su iya yin saukar kur’ani a rana guda cikin sauki

  . Karatun addu’i na ziyara daga nesa

Haka nan kuma mutum zai iya zabar karatun kashi daya bisa hudu na izihi guda a kowace rana.

Za a iya sauke manhajar ta hanyoyin:

Wayar salula mai tsaro IOS

Wayar salula mai tsarin Android

3938481

 

captcha