IQNA

Musulmin New Jersey Suna Gab da Kammala Gina Babban Masallaci

22:50 - December 01, 2020
Lambar Labari: 3485420
Tehran (IQNA) musulmin birnin New Jersey na kasar Amurka suna gina wani babban masallaci domin gudanar da harkokinsu na addini.

Shafin yada labarai na NJ ya bayar da rahoton cewa, musulmin birnin New Jersey na kasar Amurka suna  cikin gina wani babban masallaci domin gudanar da harkokinsu na addini.

Rahoton ya ce wannan masallaci zai kunshi bangarori aba-daban, baya ga wurin yin salla, zai kuma kunshi makaranta domin koyar da musulmi, kamar yadda kuma zai kunshi dakin karatu da kuma wurin ayiye ababen hawa.

Arshad Chatha shugaban cibiyar musulmi a birnin ya bayyana cewa, samun bababn wuri da musulmi za su rika gudanar da harkokinsu na addini a birnin ya zama wajibi, bisa la'akari da yadda suke karuwa.

Ya ce daga shekara ta 1980 ya zuwa yanzu, adadin musulmi mazauna birnin New Jersey ya ninka har sau uku.

3938491

 

 

captcha