IQNA

Fito Na Fito Tsakanin Al’ummar Aljeriya Da Kuma ‘Yan Mulkin Mallakar Faransa

23:42 - December 07, 2020
Lambar Labari: 3485436
Tehran (IQNA) Sheikh Bashir Ibrahimi daya ne daga cikin malamai da suka taka rawar gani wajen fatattakar Faransawa ‘yan mulkin mallaka daga kasar Aljeriya.

A cikin wani rahoto na musamman da tashar Aljazeera ta bayar, ta bayyana yadda kasar Faransa ta yi amfani da hanyoyi na rashin ‘yan adamtaka wajen azabtar da al’ummar kasar Aljeriya, a lokacin da ta mamaye kasar tare da yi mata mulkin mallaka.

Faransa ta azabtar da jama’a tare da yi musu kisan kiyashi a kasar Aljeriya, ta rika kashe mutane tamkar dabbobi, sojojinta sun rika yi wa mata fyade, sun rika wawure dukiyoyi na jama’a da kuma wadanda suke mallakin al’ummar kasa ne, tare da bautar da jama’a da karfin bindiga.

Irin wannan yanayin ne ya sanya wasu daga cikin masana da kuma malamai suka mike wajen fadakar da mutane da zaburar da su kan su mike su kalubalancin mulkin mallakar turawan Faransa, duk da cewa irin wadannan malamai da masana da dama daga cikinsu bas u tsira ba, domin kuwa Faransa ta rika bi daya bayan tana halaka su.

Sheikh Bashir Ibrahimi wanda aka haife shi a garin Qustantiniya a shekara ta 1889, daya ne daga cikin manayna malamai da suka bayar da irin wanann gudnmawa ga al’ummar Aljeriya, ta hanyar wayar da kansu a bayanansa da kuma rubuce-rubucensa na littafai.

A cikin rubuce-rubucensa yay i kokarin nuna ma jama’ar Aljeriya cewa, babu wani abu da Faransawa za su gaya musu na kauna ko kulawa ko kare hakkinsu ko neman ci gabansu da yake gaskiya, duk abin da suke fada yaudara ce da neman samun wurin zama.

Haka nan kuma ya rika fallasa Farasa tare da tona asirinta a cikin rubuce-rubucensa, da kuma bayyana irin barnar da ta yi kuma take ci gaba da yi a kasashen da take yi wa mulkin mallaka.

Ya bayyana Faransawa a matsayin ‘yan fashi ‘yan ina da kisa marrasa tausayi ga dan adam, tare da bayyana matsayin addini kan yadda ya kamata a fuskanci irin wadannan azzalumai mashaya jinin bil adam ta hanyoyi daban-daban.

Tsayin daka da juriyar al’ummar Aljeriya da gwagwarmayarsu da suka yi da makami da karfin zuciya, sun tilasta Faransa ta kawo karshen bakin zalunci da mulkin mallakarta  a kan kasarsu, duk kuwa da kisan mutane fiye da miliyan daya da ta yi a kasar.

 

3938786

 

captcha