IQNA

Kotun Kare Kundin Tsarin Mulki A Austria Ta Soke Dokar Hana Saka Lullbi A Makarantu

21:47 - December 12, 2020
Lambar Labari: 3485454
Tehran (IQNA) kotun kare kundin tsarin mulki a kasar Austria ta bayyana dokar hana ‘yan makaranta saka hijabi ko lullubi a makarantu da cewa ta saba wa doka.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, kotun kundin tsarin mulkin kasar Austria ta bayyana cewa, dokar da firayi minista Sebastian Cruz mai tsatsauran ra’ayi ya kafa a cikin watan mayun 2019, wadda ta hana yara ‘yan makaranta saka lullbi a  makarantu da cewa, ba ta a cikin kundin tsarin mulki.

Shugaban kotun kundin tsarin mulki a kasar Austria alkali Christoph Grabenwarter ne ya sanar da haka a zantawarsa da manema labarai.

Ya ce wannan doka an kafa ne bisa bangaranci da tsatsauran ra’ayi na akida, ba bisa doka ta kasa ba, saboda haka kotun kundin tsarin mulki  ta yi nazari kan wannan batu, kuma ta soke wannan doka.

Dokar jam’iyyu masu tsatsauran ra’ayi ne da suka kafa gwamnati a cikin shekara ta 2019 suka kafa ta, da nufin hana yara mata musulmi da suke zuwa makaranta saka lullubia  kansu.

Dokar dai ta tanadi cewa, duk yarinyar da bata kai shekara 10, ba za ta shiga cikin makaranta da lullubi a kanta ba, kamar yadda kuma ba za ta sanya wasu kaya irin na addininta ba, idan kuma aka samu iyayen da suka saba wa dokar, za su biya euro 440 a matsayin tara.

3940425

 

 

 

captcha