Da yake mikawa iyalin shahidin lambar, babban hafsan hafsohin sojin kasar Iran, Janar Mohammad Baqeri, ya bayyana lambar yabon a masatyin wacce ake martaba ‘yan kasa wadanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen kare juyin juya halin musulinci da hurimi da kuma ‘yancin kasar.
Jagoran juyin juya halin musulinci na Iran, Ayyatollah Sayyid Ali Khamenei, ya karrama masanin nukiliyar nan na kasar Shahid Mohsen Fakhrizadeh, da lambar yabo ta martaba sojoji.
Haka kuma a cewar Janar Baqeri, lambar yabon it ace mafi girma da ake martaba wadanda sukayi hidima wajen samar da ci gaban kasar ta fuskar kayan soji da na’urori.
Masanin nukiliyar kasar ta Iran, Fakhrizadeh, ya yi shahada ne a ranar 27 ga watan Nuwamba da ya gabata sakamakon wani hari da aka kaiwa tawagar motocinsa a kusa da birnin Tehran.
Iran dai na mai zargin Isra’ila, da kai harin wanda ta ce an yi amfani da bindigogi wadanda aka sarrafa da tauraron dan adam, saidai har yanzu Isra’ila bata ce uffan ba kan batun.
Kasar Iran dai ta sha alwashin maida martani a lokacin da ya dace dangane da kashe wanann bababn masani a nukiliya da aka kashe.